Kwararan dalilan da su ka sa na fadi zaben 2015 – Goodluck Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana abin da ya kira kwararan dalilan da suka sa shi ya fadi zaben 2015, wanda Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya yi nasara a kan sa.

Jonathan ya ce hadama da dogon burin wasu gwamnonin PDP da idanun su ya rufe a lokacin suka koma APC daga PDP, da yadda aka rika watsa labaran kage da karairayi a kan sa da kan gwamnatin sa, su ne suka kayar da shi zabe a 2015.

Jonathan ya yi wadannan ikirari a cikin wani littafin sa da aka kaddamar a yau Talata, mai suna “My Transition Hours”, wanda a yanzu haka ana kan kaddamarwa a Abuja.

Duk da irin kokarin da tsohon shugaban kasa Jonathan da majibintan sa su ka yi domin kada littafin ya fita waje kafin a kaddamar da shi, amma sai da PREMIUM TIMES ta samu tsakuro wasu surorin da ke cikin littafin.

Jonathan ya kuma dora laifin faduwar sa zabe ga wasu manyan ‘yan Arewa wadanda suka so mulki ya koma a Arewa ko ana ha-maza-ha-mata, cewa sun kitsa masa makarkashiyar hana shi yin tazarce.

“Wasu gwamnonin da suka kammala wa’adin shekarun su takwas, sun nemi zama mataimakin shugaban kasa a zaben 2015, wasu kuma su na hankoron zama shugaban kasa. To sun san idan har na fito takara, babu wanda a cikin su zai iya cimma burin sa na zama shugaban kasa.

“Yayin da suka canja sheka zuwa APC ana kusa da fara shirye-shiryen zaben 2015, babu wanda ya damu da abin da PDP ta yi ko ta ke yi ko ba ta yi ba dangane da batun cika alkawurrran da muka dauka a jam’iyyance. Sun ki yarda da na yi tazarce saboda dogon burin su na son zuciyar su kawai. Don haka babu ruwan kowa da ayyukan da gwamnati na ta yi, su dai a kayar da ni kawai shi ne abin da ke gaban su,” Inji Jonathan a cikin littafin.

Jonathan ya kara da cewa duk da gudun kaddarar da yawancin gwamnonin da suka koma APC daga PDP suka yi, hakan bai hana a yanzu sai ga shi ana cin mutuncin su da tazarta su a cikin gwamnatin APC din da suka taimaka aka kafa.

Ya ce tuni dama wasu shugabannin Arewa na kungiyoyin dattawan yankin suka nemi hana shi zama shugaban kasa wanda dokar Najeriya ce ta ba shi wannan damar zama, a bayan babu ran tsohon shugaban kasa Umaru Yar’Adua a cikin 2010.

Jonathan ya ce duk da irin wannan barazana da suka rika nuna masa da kuma kaifin adawa, sai da ya yi nasara a zaben 2011.

“Dalilin da ya sa na fito ina wannan kururuwar a yanzu shi ne saboda dukkan tuggun da aka kitsa domin kayar da ni zabe, daga kasashen waje ne, musamman daga Amurka.

“A shekarun da na shafe ina mulki a kasar nan, an sha faman danganta ni da labarai na karairayi da sharri, musamman daga wasu farfaganda da aka rika yi min daga manyan kafafen yada labarai. Ina tabbatar muku da cewa kaf a lokacin mulki na babu wasu kwarrarrun makasan da aka rika yi min sharrin wai na aika su waje sun yi horon daukar ran manyan ‘yan adawar siyasa ta. Kuma duk karya ce, babu wani sunayen da na sa aka dauka na manyan ‘yan adawar da na shirya kakkabewa daga doron kasar nan.

“Sannan kuma maganar wasu makudan kudade har dala milyan 49.8 sun salwanta, duk karaya ce. Su kan su wadanda suka yi wannan zargin da yarfe, sun san cewa duk labaran kad-da-kanzon-kurege ne kawai.” Inji Jonathan a cikin littafin.

“Babu abin da ya fi bakanta min rai sai da aka rada wa gwamnati na ko kuma ni kai na wai “mai dakusassar kwakwalwa.” An kau da kai daga gagarimin ayyukan alherin da gwamnati na ta samar. Kada a manta fa a lokacin gwamnati na ne a cikin 2013, Najeriya ta zama mafificiyar kasar da ta fi ci gaban tattalin arziki a Afrika.

“Sannan kuma a lokacin gwamnati na dan Najeriya a karon farko ya zama shugaban Bankin Inganta Tattalin Arzikin Afrika, wato African Development Bank.” Inji Jonathan.

Share.

game da Author