Kwankwadan barasa na dakile kaifin kwakwalwar mutum fiye da busa tabar Wiwi- Bincike

0

Sakamakon binciken da wasu masana kimiya dake San Diego, CA, kasar Amurka ya nuna cewa kwankwadan barasa ko kuma giya na cutar da kwanyar mutum fiye da yadda tabar wiwi ke yi.

Masana kimiyar sun bayyana cewa babbar matsalar da amfani da barasa ke yi wa kwanyar mutum shine dakile kaifin kwakwalwa.

” Za a iya kwatanta yadda barasa ke cutar da kwanyar mutum da matsalolin dakan sami jaririn da mahaifiyarsa ta sha tabar wiwi a lokacin da take da cikin sa ko kuma da matsalolin da matasan dake amfani da wiwi ke fama da su wanda ya hada da musakanci da tabuwar hankali.

A dalilin haka ne masana kimiyyar ke kira ga matasa a duk fadin duniya da su nisanta kansa daga kwankwadan barasa don lafiyar kwakwalwar su.

Share.

game da Author