KWALARA: Mutane biyar sun rasu a jihar Gombe

0

Jami’in kiwon lafiya na jihar Gombe Nuhu Bile ya bayyana cewa mutane biyar sun rasu a dalilin kamuwa da cutar kwalara.

Bile ya ce bana mutane 13 ne suka rasa rakan su sanadiyyar kamuwa da cutar Kwalara da ya bullo a jihar sannan zuwa yanzu asibitoci sun sallami mutane 500 da suka kamu da cutar.

” A yanzu haka mutane 16 na samun kula a asibitoci.”

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne kwamishinan kiwon lafiya na jihar Gombe Kennedy Ishaya ya sanar cewa cutar kwalara ta bullo a makarantar lslamiya dake Madaki a jihar.

Ishaya ya bayyana cewa a dalilin haka dalibai uku sun rasa rasu sannan 27 na kwance a cibiyar kiwon lafiya dake Madaki.

” A cikin kwanaki uku daliban makarantar wannan Islamiya 30 sun kamu da cutar sannan daga ciki uku suka rasu.

” A yanzu haka asibitin ta sallami dalibai 15 sannan ana ci gaba da kula da sauran 12.

Ishaya ya yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da wani ya kamu da rashin lafiya ko kuma aka alamun haka cewa gwamnati ta zuba magani a asibitocin jihar.

” Sannan a tabbatar an yi amfani da tsaftataccen ruwa musamman a lokacin yin alwala domin guje wa kamuwa da cutar.

A karshe yi kira ga malaman asibiti da su kare kan su daga kamuwa da cutar suma.

Share.

game da Author