Kungiyar masana magunguna ta kasa PCN za ta inganta ayyukan mambobinta

0

Shugaban kungiyar masana magunguna ta Najeriya (PCN) Elijah Mohammed ya bayyana cewa daga yanzu kungiyar za ta dauki tsauraran matakai don inganta aiyyukkan da suke yi a fannin su.

Mohammed ya ce kungiyar ta amince da haka ne domin kawar da baragurbin ma’aikata a fannin da hana sarrafa jabun magunguna a kasar nan.

Ya ce matakan da suka dauka sun hada da tabbatar da daukan kwararrun ma’aikata, horas da dalibai yadda ake amfani da komfuta da sauran su.

Idan ba manta ba a kwanakin baya ne kungiyar masana magunguna ta Najeriya rashen jihar Delta ta rufe shagunan siyar da magani 165 a jihar.

Kungiyar ta kuma tasa keyar wasu mutane bakwai da ake zargin suna da hannu a safarar magungunan da basu da aminci.

Shugaban kungiyar Anthonia Aruya da take ganawa da manema labarai ta bayyana cewa sun rufe wadannan shaguna ne saboda karya dokokin kungiyar wanda suka hada da rashin rajista,rashin tsaftace wuraren ajiyan magungunan su, siyar da magungunan da gwamnati ta hana, siyar da magunguna ba tare da izinin likita ba ko kuma ma’aikacin kiwon lafiya da sauran su.

Aruya ta kuma kara da cewa kungiyar ta gano haka ne a dalilin binciken shagunar siyar da maganin da kungiyar kan gudanar lokaci lokaci.

Ta ce kungiyar za ta wayar da kan masu ruwa da tsakin dake fannin siyar da maguguna kan kiyayae dokokin kungiyar domin kare kiwon lafiyar mutane.

A karshe Aruya ta yi kira ga mutane da su guji siyan magani a shagunan da basu da rajista, magungunan da basu dauke da kwanakin daina aiki da dai sauran su.

Share.

game da Author