Gwamnatin Jihar Oyo ta dora wa dukkanin masallatai da coci-coci na jihar kudaden harajin da ta ce ya zama tilas a rika biya.
Kudin, kamar yadda aka rubuta kunshe cikin wani daftarin bayani kan harajin, an ce za a rika amfani da kudaden ne wajen taimaka wa jami’an tsaro domin kawo karshen aikata miyagun laifuka a jihar.
Ba masallatai da coci-coci kadai aka dora wa harajin ba, har da masana’antu da kamfanoni manya da kanana.
A cikin daftatin wanda aka raba wa manema labarai yau a Ibadan, an kayyade cewa:
Masallatai da majami’u manya, za su rika harajin naira N60,000 duk shekara. Akwai kuma matsakaicin haraji na naira dubu 40,000.00, sai kuma karamin haraji na naira dubu 20,000.
Harajin masana’antu ya kama ne daga naira N100,000.
Mataimakin Gwamna Abiodun Ajimobi ne, Moses Adeyemo ya wakilci gwamnan
Ya ce ya zama dole jihar Oyo ta tashi haiikan domin ganin.ta shawo kan masu aikata manyan laifuka da suka hada da fashi, sane, sata, shaye-shaye da sauran su.
Hukimomon tsaro da yawa suka tura wakilan su a wurin taron.
Discussion about this post