KOWANE WATA: Gwamnati na kashe naira milyan 3.5 wajen ciyarwa da kula da El-Zakzaky – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na kashe naira milyan 3.5 wajen ciyar shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zazaky, wanda ke tsare kusan shekaru uku kenan.

Ana tsare da El-Zakzaky tun cikin watan Disamba, 2015 bayan da sojoji suka kashe mabiyan sa kimanin 347.

An zargi mabiyan sa da tare hanya suka hana Hafsan Hafsoshin Kasar nan, Tukur Buratai da tawagar sa wucewa a Zaria.

Kungiyar kare hakkin jama’a sun yi tir da kisan, kuma sun shigar da kara a Kotun Duniya.

Ana tsare da El-Zakzaky da matar sa Zeenat, bayan an kashe ‘ya’yan sa hudu a wancan farmaki da sojoji suka kai gidan sa.

Sau da dama kotu tarayya na bayar da beli da kuma cewa a saki malamin, amma gwamnatin tarayya ta yi biris da wannan umarnin.

Ikirarin da Lai ya yi na ciyar da Sheikh El-Zakzaky abincin naira milyan 3.5 a kowane mako, ya zo ne a rana daya da aka sake gabatar da malamin a wata kotun Kaduna, kuma aka hana belin sa.

Wani bidiyo ne aka rika watsawa inda aka nuno Lai ya na wannan ikirari ga manema labarai.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa Lai ya yi maganar da bakin sa, amma ya umarci ‘yan jarida cewa kada su buga, magana ce kawai tsakanin sa da su, ba don su bayyana ba.

Ministan na Yada Labarai ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke gabatar da wani taron manema labarai na hadin guiwa, shi da Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda har ya sa baki a cikin raha, ya ce, “to kun ga ma da a kurkuku ya ke tsare, bai fi gwamnati ta rika kashe masa naira 500,000 a wata ba, inji Amaechi.

Lai ya ce ana kashe masa wadancan makudan kudade ne, da nufin ya nuna yadda ake kulawa da shi sosai.

Sai dai kuma dimbin jama’a sun shiga shafukan su na sada zumuntar tweeter, su na caccakar ministan.

Da yawa na cewa karya ya ke kantarawa, kamar yadda suke yawan zargin sa a yawanci kalaman da ya kan furta wajen kare muradun gwamnatin tarayya.

Idan maganar Lai gaskiya, hakan na nufin a kowace rana aka ciyar da El-Zakzaky abincin naira 115,000 kenan.

Wannan ne jama’a ke ta fadin ra’ayoyin su a soshiyal midiya su na cewa ba gaskiya ba ne.

Share.

game da Author