Kotu ta umarci majalisar Kano ta dakatar da binciken Ganduje

0

Babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta umarci majalidar dokoki na jihar Kano sa ta dakatar da ci gaba da binciken harkallar dalolin da ake zargi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da aikatawa.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne ranar Litini bisa ga karar da jami’in kungiyar ‘Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria’ Mohamed Zubair ya shigar.

Lauyan da ya shigar da karar Kalid Abdullatif ya bayyana cewa yin wannan bincike ba daidai bane kwata-kwata.

Sai dai kuma lauyan dake kare kwamitin bincike na majalisar da majalisar dokoki na jihar Mohammed Waziri ya bayyana cewa an kafa kwamitin binciken ne bisa doka.

Waziri yace har yanzu majalisar dokoki da Atone- Jana basu samu matsaya ba tun da kwamitin ta fara gudanar da binciken ta.

A karshe alkalin kotun Ahmed Badamasi ya yanke hukuncin dakatar da kwamitin daga ci gaba da gudanar da bincike har sai ta kammala wannan shari’a.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 21 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author