Kotu ta bada belin dan sandan da ya harbe ‘yar uwar tsohuwar ministan kudi

0

A jiya Juma’a ne rundunar ‘yan sanda Abuja ta gurfanar da dan sandan da ya harbe ‘yar uwan tsohuwar ministan kudi Nenadi Usman a babbar kotun tarayya dake Zuba.

Lauyan da ya shigar da karar Donatus Abah ya bayyana cewa dan sandan mai suna Inagozie Godwin ya harbe wannan yarinya mai suna Anita Akapson mai shekaru 31 a ranar 13 ga watan Oktoba a Katampe Abuja da karfe 9:45 na dare.

Abah ya yi kira ga kotun da ta gaggauta tsayar da ranar fara shari’ar wannan kara da aka shigar.

Daga nan sai lauyan dake kare Godwin, Paul Samson ya gabatar da wasu hujojin da suka nuna cewa Godwin bashi da lafiya kuma yana bukata a bada belin sa domin a yanzu haka ma bashi da lafiya.

Alkalin kotun A.O. Ebong ya bada belin Godwin kan Naira miliyan 50 da gabatar da shaidu biyu a kotun.

” Sauran sharuddan belin da Godin zai ciki sun hada da samun izinin kotu kafin ya bar kasarnan sannan ya ajiye takardun tafiyar sa wajen rajistaran kotun.

Ya kuma daga shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author