KIWON LAFIYA: Ilimantarwa da ba mata tallafi ne mafita- Minista Isaac

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa ilimantar da mata zai taimaka waje rage yawan mace-macen mata da ya addabi kasar nan.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake kaddamar da kayan aikin da kamfanin Coca-cola suka bada wa babbar asibitin kasa dake Abuja.

Adewole yace za a kuma horas da su sana’o’in hannu da samar musu jarin fara sana’a.

” Sanin kowa ne cewa rashin sani da talauci na daga cikin matsalolin dake ci wa kiwon lafiyar mata tuwo a kwarya.

” Ilimantar da su da samar musu da jari zai taimaka wajen kawar matsalolin rashin sani da talauci dake hana su samun kulan da ya kamace su.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne cibiyar ‘Development Research and Projects Centre (dRPC)’, kungiyar ‘Women in Media (WIM) da kungiyar Advocacy in Child and Family Health At Scale suka shirya taron hada kawance tsakanin gwamnati da mutane domin samar da ci gaba a aiyukkan gwamnati da gwamnatin jihar Kano ke yi musamman a fannin kiwon lafiya.

Jami’ar wannan shirin Halima Ben Umar ta bayyana cewa matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da su sun shafi fannonin ilimi da ruwa wanda idan ba an mai da hankali wajen kawar da su gaba daya ba duk sa su gurgunce.

Ta ce rashin inganta kiwon lafiyar mata da yara,yawan mace macen yara, rashin horar da ma’aikatan kiwon lafiya da rashin samar da ingantattun asibitoci a yankin karkara na cikin matsalolin da ya kamata a shawo kan su.

A karshe Halima ta ce suna sa ran cewa shirin zai samar wa gwamnati da mutanen da ake shugabanta damar tattauna hanyoyin samar da ci gaba da kuma hanyoyin kawar da matsalolin da ake fama da su a fanonin da suka shafi inganta mutane.

Share.

game da Author