Bincike ya nuna cewa Najeriya na da sama da yaruka 500 amma sai gashi a rashin koyar da su da ba a yi a hankali wadannan harsuna sun kare inda yanzu yaruka 250 ne kawai ake da su a kasar.
Idan gwamnati da mutane basu mai da hankulan su ba sauran harsuna 250 da suka rage za su zama tarihi sai dai harsunan Hausa, Igbo da Yarbanci ne kawai za su rage nan gaba.
PREMIUM TIMES ta zazzagaya garin Abuja domin samun bayanan dalilan da hakan ke faruwa inda sakamakon wannan binciken ya nuna cewa mafi yawan iyaye na kin koya wa ‘ya’yan su harsunan su na asali.
Daya daga cikin matsalolin dake kawo hakan shine iyaye na son ‘ya’yan su iya turanci ne ba yarukan su ba. suna ganin yin haka burgewa wa.
Blessing Okoro mai shekaru 10 ta koka da yadda bata iya harshen mahaifin ta ba wato yaren Igbo.
Ta ce mahaifinta ba ya musu yare sai turanci. Gashi yanzu basu iya yaren ba. Sai dai da yake uwarsu yar kabilar Idoma ne ta koya musu yaren duk sun iya.
Wannan matsala ya zamo ruwan dare a musamman buranen kasar nan domin iyaye kan ga cewa wai burgewa ne ya’yan su su iya musamman turanci basu iya yaren su ba. A hankali hakan yasa wasu yarukan na bacewa domin babu masu yin su.
Masana da dama sun yi kira ga iyaye cewa ba burgewa bane kace dan ka wai sai turanci kawai, koyar da yara yarukan iyaye ba zai hana su iya wani yare da suke da burin ‘ya’yan su su iya ba. Hakan zai sa al’adu na gargajiya ya ci gaba da wanzuwa sannan yaro zai girma ya san asalin sa da al’adan sa.
Discussion about this post