Kebbi ta hada hannu da Kungiya mai zaman kanta domin tallafawa Almajirai a jihar

0

A ranar Laraba ne kwamishinan mata na jihar Kebbi Tsahara Bawa ta bayyana cewa gwamnati ta hada hannu da kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Almajiris Support Initiative of Nigeria (ASIN)’ domin ganin yadda za a iya kawar da matsalolin da almajirai kan yi faa dasu a jihar.

Bawa ta fadi haka ne a ziyarar da ‘yan kungiyar ASIN suka ziyarce ta a Birnin Kebbi.

Ta ce Almajirci a jihar na fama da matsaloli da dama wanda idan ba an gaggauta daukan mataki ba zai iya kawo wa jihar matsala matuka.

Bawa ta kuma yi kira ga mutane musamman masu fada a ji da a hana hannu da gwamnati domin ganin an kawar da wadannan matsaloli ganin cewa wasu matsalolin sun shafi addini da al’adan da mutane suka rayu a kai.

Bayan haka shugaban kungiyar ASIN Shehu Umar ya bayyana cewa inganta rayuwar almajirai, samar musu da ilimin boko da na Islama da kiwon lafiya na cikin matakan da za su taimaka wajen kawar da matsalolin da ya mamaye almajirci a jihar.

Umar ya kuma kara da cewa kungiyar su ta bude wuri domin horas da malamai da almajirai sana’o’in hannu domin su sami abin dogaro da bayan sun kammala karatunsu.

A karshe ya yi kira ga mutane musamman attajirai da su mara wa kungiyar baya bisa wannan aiki da ta a gaba.

Share.

game da Author