Kashi 70 bisa 100 na wadanda zan yi aiki da idan na doke Buhari matasa ne da mata – Atiku

0

Dan takarar shugabancin kasar nan, Atiku Abubakar ya bayyana wa gungun matasa da suka ziyarce shi a garin Yola jihar Adamawa cewa su kwantar da hankalin su idan ya doke Buhari a zabe mai zuwa, matasa da mata ne zai fi yin aiki da a gwamnatin sa.

Ya ce akalla matasa da mata ne za su kwashe kashi 70 na nade-naden da zai yi.

Su dai wadannan matasa sun kawo wa Atiku wannan ziyara ne domin jaddada masa goyon bayan su a gareshi bisa ga zabe mai zuwa.

” Kashi 40 bisa 100, matasa zan nada, sannan kashi 30 bisa 100 zan nada mata ne. Allah ya riga yayi mini gyadar dogo domin tabarkalla kam. Amma kune nake tausaya wa. Idan baku fito kun zabi PDP ba to karshen ta haka zaku ci gaba da zama cikin kunci da wahala.

” Ku tabbata ranar zabe kun fito kun yi zabe kuma ku kasa, ku tsare sannan ku raka.”

Share.

game da Author