Karnuka na iya gane zazzabin cizon sauro a jikin mutum – Bincike

0

Wasu likitoci a kasar Britaniya sun gano cewa za a iya amfani da karnuka domin gano cutar zazzabin cizon sauro a jikin mutum musamman idan alamun cutar ba su fara nunawa ba.

Likitocin sun bayyana cewa karnuka na iya gano cutar ne idan suka sunsuna jikin mutum kawai.

” Mun kawo safar kafar yara daga shekaru 5 zuwa 14 domin karnukan da muka horas su sunsuna domin gano ko wadannan yara na dauke da cutar. Ingancin sakamakon da muka samu ya kai kashi 70 bisa 100 bayan haka.

Likitocin sun bayyana cewa sakamakon da suka samu ya nuna cewa horar da karnuka domin gano ciwon zazzabin cizon sauro zai taimaka wajen ceto rayukan mutane musamman yara kanana.

Share.

game da Author