Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa kusan gwamnonin kasar nan kalilan ne za su iya biyan albashi mafi kankanta na naira 30,000.
Ya yi wannan kalamin a Abakaliki, babban birnin jihar, yayin da ya ke kaddamar da kwamitin mutane 36 da za su duba yanayi da yiwuwar karin albashi a jihar.
“Kashi 95 bisa 100 na jihohin Najeriya ba su iya biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, idan ma sun ce za su iya, burga ce kawai.
“Idan ba a kara wa jihohi kudin da gwamnatin tarayya ke ba su a duk wata ba, babu yadda za a yi su iya kara albashi.
“A kowane wata gwamnatin tarayya na kwasar kashi 52 bisa 100 na kudaden shigar gwamnati. To a lokacin da na yi kokarin lissafa cewa bari na kididdiga idan na ce kananan hukumomi su biya naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, sai na gano cewa a duk wata sai sun ramto naira bilyan 1 sun cika domin su biya albashi.
“Ni dai ba zan taba zama gwamnan da ke daukar kudaden shiga daga gwamnatin tarayya kacokan gaba daya ina biyan albashi da su ba.
“Sai an sake duba batun biyan kudin tallafin man fetur sosai, a kasar nan, watau ‘subsidy’. Idan ana so a fahimci wani abu daga ribar danyen mai. Wannan gaskiya ce, amma sai wanda ya daure zai iya furta ta, domin idan mu na adana kudaden tallafin man fetur, to za a fahimci alherin abin.
“Misali, idan aka ba ni ko aka ba jiha ta litar mai 100,000, kuma aka cire kudin ta daga kudaden da gwamnatin tarayya ke ba jiha ta a kowane wata, to kun ga kenan ruwa na ne na tabbatar da cewa mun raba mai, mun saida mun dawo da kudaden mu, ba tare da mun yi sakaci an karkatar da fetur din ba.
“Maganar karin albashin nan fa tamkar ma’aikata da kuma shugabannin kwadago na zuba ruwa ne a cikin hudajjen kwando, sannan kuma su rika addu’a wai suna so Allah ya bar musu ruwan a cikin Kwando, kada su zube a kasa.”