Karancin likitocin warkar da cutar daji na kawo cikas a fannin kiwon lafiyar kasar nan -Likita

0

Mataimakin shugaban kungiyar likitocin cutar daji (ARIN) Kamaldeen Jimoh ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance karancin likitocin cutar dajin da fannin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da shi.

Jimoh ya bayyana cewa likitocin da suka kware a warkar da masu fama cutar daji a kasar nan guda 400 ne kawai sannan idan aka kwatanta yawan mutanen dake fama da wannan cuta a kasar nan hakan yayi karanci matuka.

Ya ce a dalilin haka likitoci da marasa lafiya da dama ke ficewa kasar domin neman magani.

A karshe Jimoh yace karo ma’aikata, biyan likitoci albashi mai tsoka, samar da ingantattun kayan aiki da sauran su zai taimaka wajen magance wannan matsala a kasar nan.

Share.

game da Author