KANKANTAR ALBASHI: Fadar Shugaban Kasa ta musanta amincewar Buhari da biyan naira 30,000

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an yi wa jawabin Shugaba Muhammadu Buhari karkatacciyar fahimta, dangane da abin da ya furta a lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Sake Duba Yiwuwar Karin Mafi Kankantar Albashi.

Wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa Buhari ya ce amince da karin zuwa naira 30,000 daga naira 18,000.

Sun ce ya yi wannan kalami ne a lokacin da ya ke karbar rahoto daga shugabar kwamiti, Anne Pepple jiya Talata a Fadar Shugaban Kasa.

Sai dai kuma wata majiyar mu da ke cikin fadar shugaban kasa, wadda ta ce kada a buga sunan ta, ta tabbatar da cewa Buhari bai furta cewa ya amince da a biya naira 30,000 mafi kankantar albashi ba.

Ya dai ce Buhari cewa ya yi zai maida karfi sosai wajen aiwatar da tsarin sabon karin kudaden albashi mafi kankanta.

“Ai an fa raba da kuma yada jawabin shugaban kasa a kafafen yada labarai, jim kadan bayan ya kammala jawabin. Babu inda ya furta cewa ya amince kuma ya sa hannu a kan batun takamaimen kari zuwa naira 30,000.

“Zai yi kyau sosai mu guji yi wa rubutaccen jawabi birkitacciyar fassara.

“Tsarin mu kuma shirin mu shi ne aika wa Majalisar Tarayya sabuwar dokar mafi kankantar albashi nan ba dadewa ba.”

Daga nan a cikin jawabin, Buhari ya nemi a dan kara hakurin bai wa gwamnati uziri na wasu ‘yan makonni domin mika kudirin dokar a Majalisar Tarayya, inda za a amince da shi har ya zama doka.

Share.

game da Author