KANJAMAU: Mutane miliyan biyu ke zuwa asibiti don karbar magani a Najeriya – Hukumar NACA

0

Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau na kasa (NACA) ta bayyana cewa mutane miliyan biyu ne ke karban maganin cutar kanjamau a Najeriya.

Jami’in hukumar Gregoary Ashefor ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a jihar Legas.

Ashefor ya bayyana cewa hukumar ta sami masaniya game da haka ne bisa ga sakamakon binciken da ta gudanar a watan Yuni 2018.

Ya kuma ce wadannan mutane na samun magungunan cutar Kanjamau ne a dalilin tallafin da Najeriya ke samu daga kungiyar PEPFAR, Asussun duniya da gidauniyyar AIDS Healthcare.

Ashefor yace a yanzu haka gwamnati ta dauki wasu matakan da za su taimaka mata wajen rage yawan dogaro a tallafin da take samu daga kungiyoyin bada tallafi.

” Gwamnati na kula da mutane 76,000 dake dauke da cutar Kanjamau a jihohin Taraba da Abia sannan tana kokarin ganin ta karo yawan mutane 50,000.

A karshe Ashefor yace gwamnati za ta hada hannu da asibitoci masu zaman kan su domin sanin adadin yawan mutanen dake fama da cutar a kasar nan da kuma kokarin da fannin ke yi wajen hana yaduwar cutar.

Share.

game da Author