Shugaban Kungiyar Masana Yanayin Kasa, Ehidiamhen Charles, ya bayyana cewa jijijigar kasar da ta faru a Abuja har sau biyu, ba za ta rikide ta zama girgizar kasa ba.
Haka Charles ya furta a Minna, babban birnin jihar Neja a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
“Wadannan jijjigar kasa guda biyu kada su tayar da hankulan jama’a mazauna Babban Birnin Tarayya da kewaye.
“Jijjiga ce kawai kasa ta yi, ba wani abin damuwar da har za a yi tunanin cewa wata rana za a yi girgizar kasa ba ne.”
Ya kara cewa an shiga wani yanayi ne kawai da kasa ta dan motsa, ko kuma ta dan zakuda, amma ba girgizar kasa ba ce, kuma ba alamomin girgizar kasa ba ne.
Charles ya ce ba bakon abu ba ne idan kasa ta yi ‘yar zakuda. Kuma Najeriya ba ta a cikin yankin da girgizar kasa ka iya barkewa.
“Kai ko aman dutse ma, ba abu ba ne da ka iya faruwa a yankin Abuja. Saboda a wannan yankin babu alamomin afkuwar haka.
Ya danganta jijjigar kasa da aka yi Abuja sau biyu da cewa sun faru ne sakamakon ayyukan ginar rijiyoyin burtsatse, fasa dutse da nakiya da ake yi da kuma sauran ayyukan ginar kasa.
Discussion about this post