Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa jam’iyyun siyasa 56 daga cikin 91 masu rajista ne suka shirya shiga zaben da za a gudanar a ciikin 2019 a kasar nan.
Kwamishinan Zabe na Jihar Ribas, Obo Effanga ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fatakwal.
Ya ce INEC na sa-ido ne kan jam’iyyu 91, amma za ta maida hankali ne kawai a kan wadanda suka yi rajistar shiga zaben 2019.
Daga nan sai ya tabbatar wa jama’a cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe, za ta yi adalci kuma zaben zai zama karbabbe kuma ingantacce.
Ya jaddada yin amfani da na’urar tantance mai rajista, waro ‘Card Reader’ a zaben 2019, ya na mai cewa idan ba ta tantance mai jefa kuri’a ba, to ba zai iya yin zabe ba.