Jamilu ya fado daga Falwaya wajen lika hotunan Buhari da Badaru a Jigawa

0

A yau Laraba ne kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Jigawa Audu Jingiri ya bayyana yadda wutan lantarki ta yi ajalin wani matashi mai suna Jamilu Tukur a kauyen Kudai dake karamar hukumar Dutse.

Jingiri ya bayyana cewa Jamilu mai shekaru 27 ya gamu da ajalin sa ne a ranar Asabar bayan ya haura saman falwaya don manna hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Mohammad Badaru.

Wani mazaunin kauyen Kudai mai suna Nasiru Sani ne ya sanar wa ‘yan sanda rasuwar Jamilu.

” Ya bayyana mana cewa garin manna wannan fosta ne ya damki wayar wuta nan take ko ya fado kasa tim. An yi kokari garzaya wa da shi asibiti maza-maza a Dutse amma inaa, kafin a iya wani abu yace ga garinku nan.

Da yake juyayin mutuwar babbar dansa, mahaifin Jamilu, Tukur yace wannan kaddara ce daga wajen Allah. Ya ce dan sa yaro ne mai hankali da kirkin gaske.

A karshe Tukur ya mika godiyyar sa na musamman ga gwamna Badaru da karamar hukumar Dutse bisa ta’aziyya da suka yi masa da kyaututtuka na kudi da abinci da suka bashi.

Share.

game da Author