JAMA’A A KULA: Yanzu ana zuba maganin kashe kwari a cikin waken

0

Shugaban hukumar kula da abinci ta Kasa (CPC) Babatunde Irukera ya yi kira ga mutanen Najeriya da suyi hattara da waken da ake ci yanzu domin ana zuba masa maganin kashe kwari dake da hadari ka lafiyar mutum.

Irukera ya fadi haka wa PREMIUM TIMES a takarda da ta fito daga ofishin sa ranar Juma’a.

Ya ce ‘yan kasuwa na amfani da maganin kashe kwari mai hadarin gaske da ake kira ‘Sniper’ a cikin wake don hana wake kamuwa da kwari.

Shi wannan maganin kwari na da illa matuka a jikin mutum.

A dalilin haka Irukera yake kira ga mutane da su ringa kula da irin waken da za su siya a kasuwa kafin su ci.

Ya hori mutane da a rika dafa awake da kyau tukunna, ” misali a rika dafa wake sau biyu ana zubar da ruwan har sau biyu, sannan a hada abincin maimakon a hada tun da farko.”

Sannan kuma ya ce hukumar sa za ta ci gaba da yi wa ‘yan kasuwa kasheji bisa wannan hakan.

Share.

game da Author