Inganta kiwon lafiyar mata da yara ne mafita – Aisha Buhari

0

Gidauniyar uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ya shirya taro domin wayar da kan matan gwamnonin kasar nan hanyoyin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana.

Taron ya gudana ne a gidan gwamantin jihar Edo inda Aisha ta hori mata kan daukan tsauraran matakan da za su taimaka wajen rage yawan mace-macen yara da mata a Najeriya.

Aisha ta ce rashin yin haka ne zai kara dulmuya kasar nan cikin matsalar mutuwar mata da yara kanana.

” A dalilin haka na ke kira ga kowace matan gwamna a wannan taro da ta maida hankali wajen wannan shiri.

Share.

game da Author