INEC ta yi wa ma’aikatan ta 2,209 karin girma

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi karin girman matsayi ga ma’aikatan ta su 2,209.

Ta yi musu karin girman ne bayan da ta gudanar da jarabawar neman karin girma ta shekarar 2018.

INEC ta sanar da haka ne a cikin wata takardar manema labarai da Kwamishina na Kasa kuma Mamba na Kwamitin Wayar da Kan Jama’a a kan Zabuka, Muhammed Haruna ya saw a hannu a jiya Alhamis.

Haruna y ace an kara wa kananan ma’aikatan INEC 847 girman matakai, yayin da manyan ma’aikata su 1,362 suka samu wannan gusawa gaba daga matakan da su ke.

“Daga cikin kananan ma’aikata 927 da suka rubuta jarabawar, 847 ne suka samu nasara, yayin a cikin 1847 na manyan ma’aikata, aka yi wa 1,362 karin mataki.

Ya kuma ce takwas daga cikin manyan ma’aikatan sun samu mukamin darakta a wannan jarabawa ta karin girma da aka gudanar.

A wani labarin kuma, INEC ta bayyana cewa gudanar da dukkanin zabuka a rana daya ya fi saukin kashe kudi, idan aka yi la’akari da yadda ake kashe makudan kudade wajen gudanar da zabe.

Kwamishinar Zabe ta Kasa Amina Zakari ce ta bayyana haka a taron ta da shugabannin kungiyar masu motocin haya, wato NARTO, a Abuja.

Ta bayyana musu cewa zaben 2019 zai ci kudi har naira bilyan 85 wajen zirga-zirga, safarar kayan aiki da kayan zabe a kowane lungun kasar nan, da sauran aikace-aikace na kai-da-kawo.

Ta kara da cewa matsalar tsaro da rashin kyawon wasu hanyoyin kasar nan na daga cikin dalilan tsadar ayyukan zirga-zirgar.

Dangane da yankunan da tilas sai an shiga ruwa kuwa, Amina ta ce kudaden da ta lissafa ba su shafi wasu shafi wasu kudaden da aka ware domin hayar kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a yankunan da ke kewaye da ruwa ba.

Inji ta, akwai kuma batun kananan jiragen ruwa na jami’an tsaro, daukar hayar helikwafta a yankunan da ta’addanci ya yi kaka-gida da sauran su.

Ta ce ana ta wannan kokari ne domin ganin cewa an isar da kayan zabe a ko’ina, tsakanin 5:30 na safe zuwa 8:00 na safe.

Share.

game da Author