Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta sa ranar 17 Ga Nuwamba, za a gudanar da zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya/Ingawa/Kusada.
Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa za a yi takarar kujerar ne bayan da dan majalisar da ke a kai a baya, Ahmed Kata, ya sauka ya tsaya takarar sanatan Katsina ta Arewa, kuma yayi nasara.
Kaita ya nemi takarar sanatan ne bayan rasuwar Mustapha Bukar, watanni shida da suka gabata.
Jami’in wayar da kai na INEC a Katsina, Mohammed Takai ne ya bayyana ranar da za a gudanar da zaben, cewa za ta kama ranar Laraba, kuma hukumar su ta lika wannan sanarwa a dukkan kananan hukumomin uku.
“Tuni mun dauki ma’aikata na wucin gadi wadanda za su yi aikin zabe, kuma mun gana da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin nasara.
Discussion about this post