Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta danganta tsadar kashe kudade wajen gudanar da zabe a kan matsalar tsaron da ake fama da ita a fadin kasar nan.
Wannan ne ya na INEC ta yi kira da a zauna lafiya a cikin kauna da amintakar zamantakewa a kasar nan.
Kwamishinan Tarayya mai kula da Enugu, Benuwai da Anambra, Festus Okoye ne ya yi wannan tsokacin a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin siyasa da kungiyoyi da ‘yan jaridu a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.
Ya jaddada cewa duk da dai ana samun wanzar da zaman lafiya idan aka tura jami’an tsaro a lokutan zabe, ya kuma yi nuni da cewa aikin raba jami’an tsaron ya na cin makudan kudade sosai.
Ya ce hukumar na kokarin tabbatar da cewa wadanda ke zaune a sansanonin masu gudun hijira duk wanda ke da rajista ya yi zaben 2019.
“Yanayin masu zaune a sansanonin gudun hijira abin takaici da tausayawa ne matuka. Ba wanda zai yi fatan ya samu kan sa zaune a sansanin masu gudun hijira. Ina kara yin kira ga kafafen yada labarai su ci gaba da wayar wa jama’a kai game da illa da masifar ta’addanci.”
Ya ce duk da irin mawuyacin halin da mazauna sansanonin gudun hijira ke ciki, INEC za ta tabbatar da cewa su ma sun jefa kuri’a a zaben 2019.
Discussion about this post