Odita -janar na kasa Anthony Ayine ya zargi hukumar yaki da hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) da kin samar wa hukumar bayanan takardun yadda ta kashe kudadenta daga 2015 zuwa 2018.
Ayine ya ce hakan da NACA ta yi ya saba wa tsarin dokokin Najeriya da tsarin dokokin aikin tattance takardun bayanan kudade na ofishin Odita janar din.
” Mun nemi hukumar ta bamu takardun bayanan yadda ta kashe kudaden ta ganin cewa kungiyoyin da ke ba Najeriya tallafi na shirin dakaktar da tallafin da su ke ba kasar.
” Kungiyoyin sun koka da yadda Najeriya ke kin amfani da kudaden da take samu domin tallafi ga cutar Kanjamau da sauran su.
A dalilin haka Ayine yake kira ga shugaban hukumar Sani Aliyu da ya mika wa hukumar cikakken bayanai domin gudanar da bincken.
Aliyu ya ce ofishin Odita – Janar ba za ta sami wadannan takardu ba saboda ofishin sa basu ajiyan irin wadannan takardu. Ya ce abin da suke yi a ofishin su shine yin da aiyukkan da ya kamata hukumar ta aiwatar kawai.
A karshe Aliyu yace yana da shaidar sakon da ya aika wa ofishin Odita-janar kan inda zai sami wadannan takardu da sauran bayanan da yake bukata.