Hukumar Abinci ta Duniya, FAO ta raba risho 11,000 ga ‘yan gudun hijira a Barno

0

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (FAO), ta bayyana cewa ta raba risho na girki ga iyalai 11,000 da hare-haren Boko Haram ya kora ko ya tarwatsa gidajen su a jihar Barno.

Jami’ar yada labarai ta FAO ce mai suna Patricia Pink ta bayyana haka a cikin wata takardar da ta raba wa manema labarai a jiya Laraba, cewa an raba shi ne a karkashin daukar nauyin Shirin Samar da Murhu Mai Amfani da Mai, wato SAFE, da gwamnatin kasar Norway ta dauki nauyi.

Pink ta ce tuni mutane 5,000 suka amfana da shirin, yayin da wasu 6,000 kuma za su ci gajiyar wadanda za a raba musu nan da karshen watan Disamba.

Ta ce shirin ya ta’allaka ne a kokarin ganin an wadata masu karamin karfi da risho din mai aiki da mai, sannan kuma a kawo karshen yin amfani da itace wajen girke-girken abinci, wanda shi ke haifar da asarar itatuwa a cikin dazuka.

Pink ta ce sare itatuwa na kara matso da Hamada kusa.

Sannan kuma Pink ta ce risho din a nan jihar Barno ake yin sa, inda kungiyar su ta kafa masana’antar yin risho din a Maiduguri, Jere da Konduga, kuma ta dauki matasan da suke aikin hada risho din har su 100.

Share.

game da Author