Kwamitin Binciken da Majalisar Jihar Kano ta kafa domin binciken zargin karbar rashawar dala miliyan da aka yi wa Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje, ya gayyaci Ganduje da ya gurfana a gaban sa.
An umarci gwamnan ne da ya kai kan sa a ranar Juma’a, domin amsa tukhumar binciken da ake masa, wanda wata jarida mai suna Daily Nigerian ta buga.
Badakalar ta samo asali ne tun bayan da jaridar ta buga bidiyon Ganduje ya na karbar kudaden rashawa daga hannun ‘yan kwangila.
Sakataren kwamitin binciken, Mustapha Soron Dinki, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa an tura wa Ganduje wasikar tun ranar Labara.
Shugaban Kwamitin ne, Baffa Babba Dan’agundi ya sa wa wasikar gayyatar hannu, inda aka ce ya zo ya masa wasu tambayoyi dangane da batun zargin sa da ake yi.
An kuma ba shi zabin cewa idan ya ga dama zai iya halartar zauren kwamitin bincken tare da lauyoyin sa.
Tun ranar 25 Ga Oktoba, Editan Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya bar Abuja, ya je Kano ya amsa tambayoyi daga bakin ‘yan kwamitin binciken su bakwai.