#HARKALLAR DALOLI: Ganduje ya ki amsa gayyatar kwamitin bincike na majalisar jiha

0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya ki amsa gayyatar da kwamitin majalisar jihar ya kafa na mutum bakwai da za su binciki zargin karbar rashawar da aka yi masa.

Jaridar Daily Nigerian ce tafallasa bidiyon da aka nuno Ganduje na karba milyoyin daloli daga hannun ‘yan kwangila, wadanda aka kiyasta sun kai dala milyan biyar.

Ganduje ya karyata zargin, inda ita kuma majalisar jihar Kano ta kafa kwamitin bincike.

Zaman farko dai kwamiti ya gayyaci mawallafin jaridar, Jaafar Jaafar, kuma ya haklarta, inda ya kara jaddada sahihancin bidiyon.

A nasa bangaren, maimakon Ganduje ya halarta da kan sa, ya tura Kwamishinan Yada Labarai, Muhammed Garba ya wakilce shi.

Yayin da ya ke wa kwamiti jawabi bayan ya damka rubutaccen bayani ga shugaban kwamiti, Baffa-Dan’agundi, Garba ya ce zargin da aka yi wa gwamnan ba gaskiya ba ne, kuma ya sosa masa rai sosai.

“Mai Girma Gwamna ya karyata zargin da aka yi masa. Bai karbi rashawa ba kuma ba zai taba karbar rashawa ba. Wannan zargi ya ci zarafi da mutuncin gwamna sosai.” Inji Garba.

Garba ya shawarci kwamiti da ya yi aikin sa tsakani da Allah.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Ibrahim Muktar, ya jinjina wa kwamitn dangane da yadda ba su nuna son kai a bangaren wanda ake zargi da kuma wanda ya yi zargi.

Lauyan Ganduje mai suna Ma’aruf Yakasai, ya ce gwamna ya zabi ya tura wakilci ne maimakon ya je da kan sa, kuma ya ce tun farko gwamnan na da ‘yancin da zai maka Daily Nigerian kotu, amma sai ya kyale majalisa ta yi aikin ta.

Shugaban Kwamitin, Baffa Dan’agundi ya ce nan gaba za a kira kwararru wadanda za su kalli bidiyon a gaban lauyan Ganduje da na Jaafar sannan su tabbatar da sahihancin su ko akasin haka.

Sai dai ya ce a kebantaccen wuri ne za a yi wannan aikin tantancewar.

Share.

game da Author