Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya tsunduma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a cikin wadanda suka yi masa taron-dangin kayar da shi zaben 2015.
PDP a karkashin Jonathan ta sha kaye a zaben da aka gudanar, 29 Ga Maris, 2015, wanda ya kawo a karon farko jam’iyyar adawa ta kafa gwamnati a Najeriya.
A cikin littafin sa da aka kaddamar jiya Talata a Abuja, Jonathan ya ce Jega ta taimaka wajen nuna son kai a rabon kayan zabe a zaben da aka gudanar ranar 28 Ga Maris, 2015.
“Saboda dalilai na son kai, INEC ta raba kayan zaben musamman katin zabe, PVC a dukkan ilahirin fadin Arewacin kasar nan, har da yankin Arewa maso Gabas, inda Boko Haram suka yi katutu. Amma ta kasa rarraba wadannan katin zabe a yankin kudancin kasar nan, inda za a iya cewa can ne ma ya fi Arewa zaman lafiya a lokacin.
Jonathan ya kara da cewa, ya maida hankalin sa sosai a lokacin da aka rika bada rahotannin kumbiya-kunbiya da magudi a wurin zabe, amma sai bai biye ba, kuma bai yi amfani da wadannan rahotanni da kafafen yada labarai suka rika bayarwa ba, balle ya kekasa kasa ya ce bai amince da zaben ba.
“An rika watsa labarai iri daban-daban a soshiyal midiya da hotuna da bidiyo da dama na yadda aka yi ba daidai ba a wurare da yawa lokacin zabe. Kawai dai sai na bar wa zuciya ta cewa ba zan ci gaba da kasancewa shugaban kasa ba, saboda irin yadda aka yika tafka rashin daidai da adawa da kuma abin da INEC ta yi, hukumar da ni ne na karfafa ta na kuma inganta ta.
“Duk duniya ta ga halin da na tsinci kai na har a cikin yankin mu, inda na je zabe a mazabar garin mu, amma na’ura ta ki tantance ni duk kuwa da irin kokarin da na yi ta yi ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
“Abin mamaki, haka aka yi wa mata ta da kuma mahaifiya ta. Dukkan su na’urar INEC ta kasa tantance su. Wannan ya nuna kuma ya fallasa kasawar INEC matuka.” Inji Jonathan.
Jonathan ya ci gaba da cewa duk da dai ya amince da an kayar da shi ne kuma ya karbi kaddara saboda nagartar halayyar sa, ya kuma amince ne domin gudun kada mummunar fatar da Amurka ta yi wa Najeriya, cewa za ta tarwatse ta tabbata.
Ya kuma ce ya amince ne saboda kada mummunan furucin da Buhari ya yi cewa “za a yi kare-jini-biri-jini” ya tabbata.
“tun ana sauran kwana daya kafin na kira Buhari a waya na san yadda sakamakon zaben zai karke, saboda ina bibiyar rahotanni, kuma ina ganin yadda ake ta yawan samun mishkiloli a bangaren INEC.
“Amma da ya ke ni mutum ne mai son zaman lafiya, sai na kaddara cewa tsayar da zabe a ranar kada kuri’a, tamkar tayar da bam ne a cikin kasar nan.”
Jonathan ya ci gaba da cewa jim kadan bayan ya jefa kuri’a a ranar 29 Ga Maris, ya baro Bayelsa ya koma Abuja, inda ya rika bibiyar dukkan yadda zaben ke gudana a fadinn kasar nan. Har zuwa ranar 31 Ga Maris, 2015, ranar da ya kira Buhari ya taya shi murnar amincewa da kayar da ni da ya yi, tun ma kafin a INEC ta bayyana wanda ya yi nasara.
Har ila yau, Jonathan ya bayyana sunayen wasu garuruwa da ya ce ya yi gudun kada rikici ya barke idan da bai yi gaggawar kiran Buhari a waya a waccan ranar ba.
“Gaba dayan kasar nan ta dauki haramin neman barkewar tashin hankali. Sai na ga cewa ya kamata na yi wani abu cikin gaggawa. Na ce a zuciya ta ba zan tsaya na jira wai sai an kammala bayyana sakamako ba tuna. Sai kawai na dauki waya na kira Buhari, don kasa ta zauna lafiya.
“A Lagos dai jama’a kadan ya rage su barke da tashin hankali kan titina. A Arewa kuwa can dama kadan kyes ake jira komai ya dagule. A Abuja kuma daya daga cikin ejan di na, Godsday Orubebe ya shiga tankiya da hatsaniya da shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, a wurin tattara kuri’u da kidayawa.
Jonathan ya ce wadanda ke tare da shi a lokacin da ya kira Buhari ya taya shi murna, akwai tsohuwar ministar kudade, Ngozi Okonjo-Iweala, tsohon ministan shari’a, Bello Adoke, tsohon ministan sufurin jirage, Osita Chidoka, alkalin alkalai na tarayya, Mohammed Bello da mataimaki na musamman a kan harkokin cikin gidan shugaban kasa, Waripamoei Dudafa.