Haji 2019: Za a fara yi wa maniyyatan jihar Kaduna rijista daga ranar Laraba

0

Jami’in hukumar kula da jin dadin alhazai na jihar Kaduna Hussaini Tsoho -Ikara ya bayyana cewa hukumar za ta fara yi wa maniyata aikin hajin 2019 rajista ranar Laraba 21 ga watan Nuwamba.

Tsoho -Ikara ya sanar da haka ne ranar Litini a Kaduna da yake ganawa da manema labarai inda ya kara da cewa za a fara rajistan ne a duk kananan hukumomin dake jihar.

Ya kuma yi kira ga maniyyatan da su zo wakilin su wajen yin rajistan.

” Wannan karon duk wanda bai zo da kan sa ba ba za ayi masa rajista ba, mata kuma idan basu zo da muharramin su ba ba baza ayi musu rijita ba sannan idan mace mai ciki ko kuma tsohuwa suka zo wajen yin rajistan ba tare da dan rakiya ba ba za a yi musu rajista ba.

Tsoho -Ikara ya ce wannan karon maniyatan da suka taba zuwa aikin haji sau hudu zuwa kasa za su biya karin riyal 2000.

Ya ce sabbin maniyyata za su biya kudin tafiya daga Naira 800,000 zuwa miliyan daya.

Share.

game da Author