Gwamnatin jihar Legas ta amince wa dalibai mata su rika saka hijabi idan zasu zo makaranta

0

Gwamnatin jihar Legas ta amince wa daliban makarantun jihar su saka hijabi a makaranta.

Shugaban kungiyar dalibai musulmai na Najeriya (MSSN) reshen jihar Legas Saheed Ashafa ya sanar da haka.

Ya bayyana cewa gwamnati ta amince da haka ne bisa ga rahotannin tauye hakin dalibai musulman da aka dunga yi a jami’ar Ibadan dake jihar Oyo.

” Daga yanzu gwamnati ta amince wa mata musulmai su rika yafa hijabi zuwa makaranta a jihar Legas ba tare da wani ya muzguna musu ba.

Ashafa ya jinjina wa gwamnati bisa wannan kokari da tayi wa dalibai musulmai mata a jihar.

Share.

game da Author