Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Delta Ononye Mordi ya bayyana cewa ma’aikatar kiwon lafiya ta ware Naira biliyan 8.6 daga cikin kassafin kudin shekarar 2019 domin inganta fannin kiwon lafiya a jihar.
Ya sanar da haka ne ranar Litini yayin da ya gabatar da kassafin kudin fannin wa kwamitin kiwon lafiya na majalisar dokoki na jihar domin tantancewa.
Mordi ya bayyana cewa gwamnati ta ware wadannan kudade ne domin inganta kiwon lafiyar da mutanen jihar ke samu.
A karshe shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar Alphonsus Ojo ya tabbatar cewa majalisar za ta tantance kasafin kudin da ma’aikatar kiwon lafiyar ta gabatar musamman yadda hakan ya shafi inganta kiwon lafiyar mutanen jihar.