Gwamnatin Tarayya ta bayyana ce daga watan Janairu, 2019, za ta fara raba abincin tara ga makarantun firamare 626 da ke cikin kananan hukumomin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Manajar Tsare-tsaren Ciyarwar, Victoria Aleogena, a lokacin da ta ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, jiya Laraba.
Victoria, wadda kuma ita ce Mataimakiyar Daraktan Kiwon Lafiya a Sakateriyar Ilmi ta FCT, ta ce za a raba abincin ne ga yara ‘yan firamare daga makarantun gwamnati 626 da ke cikin kananan hukumomin FCT shida.
Ta ce za a rika bayar da abincin ne sau daya a rana ga ‘yan aji 1 zuwa 3 kadai.
Daga nan ta kara da cewa wadanda za a rika sayen abincin daga gare su, ana bukatar su cike wani fam bayan sun kawo hotunan su guda biyu.
Sai kuma ta yi kira ga iyaye da malaman makaranta da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na yankin, su bayar da hadin kan ganin cewa shirin ya samu nasara.