Gwamnati ta gurfanar da ‘yan Shi’ar da aka kama a kotu

0

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu daga cikin mabiya Shi’ar da ‘yan sanda suka kama a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a Abuja.

An dai kama kimanin 400 daga cikin su bayan an yi zanga-zangar da ta karke da kashe kimanin 50 daga cikin su a tsakanin Ranakun Litinin da Talata.

Sojoji ne suka bude musu wuta a ranakun biyu, a Zuba, Nyanya da kuma Dei-dei, kuma sojojin sun ce an tunzura su fara kai musu hari har da farfasa musu mota.

Mabiya Shi’a sun musanta wannan zargi, kuma kungiyar Jinkai ta Duniya, Amnesty International ta yi Allah wadai da kisan.

Daga daga cikin mambobin Shi’a mai suna Abdullahi Musa, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an gurfanar da wasu mambobin a Kotun Majistare da ke Wuse, Abuja.

Share.

game da Author