Gwamnati ta dauki mataki don dakile yaduwar cutar Noma a kasar nan

0

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Abdulaziz Abdullahi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakan da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar Noma.

Abdullahi ya fadi haka ne a taron wayar da kan mutane game da cutar Noma da aka yi a Abuja ranar Litini.

Ya bayyana cewa cutar noma cuta ce dake kama fatar mutum wanda idan ba a gaggauta daukan mataki ba ya kan sa a yanke wani bangaren jikin mutum ko kuma ya kawo ajalin sa.

Abdullahi ya ce bincike ya nuna cewa cutar ta fi kama tallakawa musamman wadanda ke zaman karkara.

” Rashin tsaftace jiki, muhalli da rashin cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar Noma.

Ya ce a yanzu haka gwamnati ta dauki matakin wayar da kan mutane da hada karfi da karfe da kungiyar kiwon lafiya ta yammacin Afrika (WAHO) don inganta asibitocin kula da masu fama da wannan cuta.

A karshe Abdullahi yace sun gano cewa hakan na cikin dabarun da za su taimaka wajen kawar da yaduwar wannan cutar ganin cewa mafi yawan mutanen dake fama da cutar basu da masaniya game da cutar da inda za su iya samun kula.

Share.

game da Author