Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara a Shirin Inganta Al’umma, Maryam Uwais, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ciyar da daliban firamare kwan kaji har milyan shida da kuma shanu 594 a kowane mako.
Ta ce ana ciyar da su wadannan adadin ne a karkashin shirin gwamnatin tarayya da ciyar da yara a makaranta.
Ta yi wannan furucin ne a Abuja a lokacin da tawagar duba da nazarin yadda gwamnatin Najeriya ke gudanar da shirin inganta al’umma ta kai mata ziyara daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
Uwais ta ce a zaman yanzu gwamnatin tarayya na ciyar da yara har milyan tara daga jihohi 26 da ke cikin jihohi 36 na kasar nan.
Shirin inji Uwais wata hanya ce da gwamnati ta bullo da ita domin zaburar da iyaye sha’awar sa yaran su makaranta.
Wannan shiri inji Uwais ya kara habbaka shirin noma da kiwo a kasar nan, domin a cewar ta, hakan ya kara habbaka kiwon kajin da ke nasa kwayaye ana saye ana ciyar da akalla kwai daya a kowane yaro a kullum.
A bangaren kiwon lafiya kuma, Uwais ta ce abincin ya na kara wa yara sinadarin gina jiki sosai, domin abinci ne mai rai da lafiya.
Ta kara da cewa ana sayen metirik tan har 83 na kifi da ake ci a kowane mako a makarantun.
Shirin inji Uwais ya kasa sama wa jama’a da dama aikin yi, kama daga masu raba abinci zuwa masu girkawa.
John Mughabushaka, wanda shi ne shugaban tawagar daga Jamhuriyar Dimokrdiyyar Congo, ya ce sun zo ne domin su ga yadda Najeriya ke yi, su ma idan sun koma gida za su kwaikwayi kamar yadda Najeriya ke yi.