GARKUWA DA MUTANE: Abu na neman ya gagari gwamnati, mutanen arewa a fa tashi da addu’a, Daga Younus Mohammed

0

Duk wani mazaunin Arewacin Najeriya zai fadi maka cewa a iya tsawon rayuwar sa a wannan yanki bai taba jin wai ana sace mutum dan Adam a ce wai sai an biya kudi kafin a sake shi sai a shekarun nan da muke ciki.

Ada dai sai dai kaji ko a kafafen yada labarai cewa irin haka na faruwa a yankin kudu ne ko kuma ma a wasu kasashe sai gashi abu kamar wasa abu ya zama ruwan dare a wannan yanki na Arewa.

Tashin hankali, mutum bai ci ba bai sha ba sai a wayi gari ana bin masallatai, makwabta da yan gari ana neman taro ko sisi domin a biya wasu ‘yan ta’adda miliyoyin kudi don an dauke maka da, ‘ya mata, koma kai kanka.

Wasu da dama sukan gamu da ajalin su a wadannan wurare wasu kuma da ke da sauran kwanaki a duniya sai Allah ya kwato su daga hannun wadannan muggan mutane.

Wasu hanyoyin ma yanzu sun fara zama kufayi domin kwata-kwata mutane sun dai na bin su. Dayawa cikin mutane a kauyuka sun daina zuwa gonaki saboda tsoron kada a sace su a saka ‘yan uwa cikin halin kakanikayi.

Wadannan masu garkuwa basu raga wa kowa. Tsawon gemun ka ba ya basu tsoro haka za su tarkata ku du auna da ku cikin kurgunmin daji zuwa har Allah ya ci da kai idan da sauran zaman ka a duniya.

Jihohin Kaduna, da zamfara sune suka fi fadawa cikin wannan matsala.

Idan ka tafi tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja, za ka mutane ta ko ina ana neman tikiti zuwa Abuja. Da yawa idan ka tambayesu za su ce maka tsoron kada ayi garkuwa da su suke yi shine yasa za su bi jirgin.

A jihar Zamfara kuwa kazamcewa abin yayi domin kuwa ba sai kabi hanya ba, a gidan ka ma kana kwance za a biyo ka a dauke ka ko ‘yayan ka. Idan sun barka da rai, an samu dacews

Yanzu ya kai ga hatta manyan jami’an gwamnati, gaggan ‘yan siyasa dake gwamnati da wadanda ma basu gwamnati sun hakura suna biyan masu garkuwan kudin fansa.

Abu dai kamar ya gagara ne ko kuwa sakaci ne na gwamnati.

A dan kwanakinnan aka saki wasu tagwaye da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara, wani sanata da shugaban karamar hukuma ne suka nemo sama da miliyan 10 a tsakanin su suka biya tare da dan kudaden da mutanen gari suka harhada domin a ceto wadannan yan mata.

Kullum sai fadi ake wai gwamnati ta tura jami’an tsaro wadannan yankuna amma duk a banza. Harkokin su suke yi babu abinda da ya dada su da kasa.

Birnin Gwari a jihar Kaduna shima ya kai ga kusan kowa ya zama mai gadin iyalan sa ne. Duk lokacin da wadannan miyagu suka ga dama sai su shigo gari abin su salin alin cikin kwanciyar hakali su dauki na dauka sannan wanda kwanan sa ya kare su harbe shi.

Wannan masifa ya zama abu ne da bai kamata a nade hannu a zuba wa gwamnati ido ba saboda ga dukkan alamu abin ya na neman ya fi karfin jami’an tsaron kasar nan koma ince ya fi.

Dole ‘yan uwa mu tashi mu shiga yi wa wadanan mutane addu’oi da Alkunutai domin Allah ya tausaya mana idan masu shiryiwa ne Allah ya shirya su, idan ba haka ba kuma Allah ya kawo mana karshen sa. A gaskiya mu rabu da ‘yan siyasar nan mu dawo mu koma ga Allah. Su fa siyasar su ce a gaban su ba kai ba. Idan ma an sace na su suna da abin biya amma kai fa?

Mutanen Arewa ba su gama fama da bala’in Boko Haram ba har yanzu sannan ga wannan masifa na masu garkuwa.

Ya Allah muke roko ya kawo mana karshen wannan damuwa. AMIN.

Share.

game da Author