FYADE: Kotu ta daure wani magidanci a Jos

0

Kotun dake Kasuwar Nama a garin Jos Jihar Filato ta daure wani magidanci Isaac Philip mai shekaru 61 a kurkuku na tsawon shekara uku a dalilin yi wa ‘yar shekara takwas fyade.

Lauyen da ya shigar da karar Ibrahim Gukwat ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar mai suna Favour Emmanuel ce ta kawo kara ofishin ‘yan sandan dake Mado Tudun-Wada a Jos ranar 9 ga watan Oktoba.

Gukwat yace bisa ga karar Favour ta zargi Philip da laifin danne ‘yarta ne a cikin gidansa bayan ya lallabe ta ta bishi cikin gidan.

Daga nan alkalin kotun Yahaya Mohammed ya yanke hukuncin daure Philip a kurkuku na tsawon shekaru uku.

Ya kuma yi watsi da rokon alfarmar sassauci da shi Philip ya nema domin ya zama abin koyi wa mutanen dake aikata irin haka ga kananan yara.

A karshe Mohammed yace Philip zai biya iyayen yarinyar Naira 20,000 kudin asibitin yarinyar.

Share.

game da Author