Kwamishinan Shari’a na jihar Kwara, Kamal Ajibade, ya bayyana cewa babban gogarman ‘yan fashin da ake zargi sun yi fashi da kashe-kashe a bankin Offa a jihar Kwara, ya mutu a hannun ’yan sanda.
Kamal Ajibade, ya shaida wa Babbar Kotun Ilorin haka yau Laraba, a lokacin da aka gabatar da sauran wadanda ake zargin su biyar a kotu.
Kwamishinan ya ce Abba Kyari, wanda shi ne Mataimakin Sufurtanda na ‘Yan sanda mai kula da ayarin masu bincike na musamman na ofishin Sufeto Janar ya shaida masa mutuwar wanda ake zargin ta wayar tarho.
Daga nan sai ya nemi a daga karar domin ya yi gyara a cikin takardar gabatar da karar wadanda aka zargin, domin ya cire wanda ya mutu din.
Ya ce mamaci ba a shigar da shi kara, don haka kafin a ci gaba da sauraren karar tilas sai an cire sunan sa.
Mai Sahari’a Halima Salman ta amince da daukaka kara zuwa ranar 30 ga Nuwamba.
Wadanda ake zargin dai sun kai hari ne a bankin First Bank na garin Offa a jihar Kwara, har suka kashe mutane 31.
An zargi Shugaban Majalisar Dattwa, Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Kwara, Fatah Ahmed, amma duk sun karyata, sun ce sharri ne da yarfen siyasa kawai.
Discussion about this post