Gwamnatin jihar Kaduna ta daga darajar masarautar Chikun daga daraja ta biyu zuwa ta daya.
Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa gwamnati ta daga darajar wannan masarauta ne ganin irin gudunmuwar da sarkin Chikun Mai martaba Danjuma Barde ya bada wajen samar da zaman lafiya a jihar Kaduna musamman a yankin da yake mulki.
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi Farfesa Kabiru Mato ne ya saka hannu a wannan karin daraja da aka yi wa wannan masarauta.
A sakon taya murna da gwamna El-Rufai ya aika wa sarkin, ya jinjina masa sannan ya hore sa da ya ci gaba da ayyukan alheri da ya ke yi wa mutanen wannan yanki na Chikun da jihar Kaduna baki daya.