Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta bayyana cewa ta kama wasu mata guda bakwai da ta samu da laifin yi wa ‘yan mata 11 kaciya.
Mai taimaka wa uwar gidan gwamnan jihar kan harkokin yada labarai Donatus Owo ya sanar da haka wa manema labarai a fadar gwamnatin jihar inda ya bayyana cewa wadannan mata sun aikata haka ne a kauyen Okpuitumo dake karamar hukumar Abakaliki.
A dalilin haka Owo ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki matakai domin karfafa dokar hana yi wa mata kaciya a jihar.
” A yanzu dai gwamnati ta kafa wani kwamiti da suka hada da shugabanin kananan hukumomi da sarakunan gargajiyya domin ganin an hana yi wa mata kaciya.
Owo ya ce bisa ga dokar da aka kafa a jihar duk wanda aka kama yana aikata haka zai biya taran naira 200,000 ko kuma zaman kurkuku na tsawon shekaru biyar ko kuma ya sha dukan tsiya.
Discussion about this post