DAWOWAR ATIKU: Jami’an SSS sun ci mutunci na a filin jirgi, Inji Atiku

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa jami’an tsaro a filin jirgin sama na Abuja.

Atiku ya rubuta a shafin sa ta Tiwita inda ya ce ” yau an yi mini binciken cin mutunci a filin jirgin saman Abuja. Jami’an tsaro sun yi mini tonon silili, ciki da bai. Buri na shine a gina kasa da jami’an tsaro ba za su rika ci wa mutanen Najeriya mutunci ba.

Idan ba a manta ba, Atiku, kuma dan takarar shugabancin Najeriya a Inuwar Jam’iyyar PDP ya fice daga kasar nan ne makonni bayan ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Atiku da wasu ‘yan jam’iyyar sun tafi kasar Dubai ne domin hutawa da kuma tattaunawa da ganawa a tsakanin su game da shirin tunkarar kamfem din da za a fara daga ranar 18 ga wannan wata na Nuwamba.

Share.

game da Author