Daruruwan mazauna garin Judumri sun arce a dalilin harin Boko Haram da yammacin Asabar

0

A yammacin Asabar din nan ne Boko Haram suka kai wa kauyen Judumri hari da yasa daruruwan mazauna garin suka arce daga garin zuwa Maiduguri.

Wani mazaunin garin ya ce tun da karfe 6 na yamma ne suka fara jin karar harbin bindiga ta ko ina a kauyen.

Sijoji da ke aiki a garin suka umurce mu da mu fice daga kauyen kafin.

Wakilin PREMIUM TIMES ya shaida wa mana cewa zuwa yanzu ya ga tulin motocin sojoji da na ‘yan sanda suna kokarin shiga garin domin dakile wannan hari.

Share.

game da Author