Wani abin al’ajabi da ya auku a jihar Anambara ranar Asabar ya dade yana ba mutane mamaki da yin juyayi.
Wani magidanci ne mai shekaru 65 ya rasu a daidai yana tare da budurwar sa a dakin Otel suna holewa.
Ita dai budurwar sa ta nemi ra sulale ne daga dakin Otel din bayan ta ga alamar mutumin baya motsi sai ko ma’aikatan Otel din suka tambaye ta ina wanda suka shiga dakin tare.
Daga nan ne fa aka bita ciki sai suka ganshi rashe-rashe a kwance ba ya iya motsi.
Sai ko suka sanar wa ‘Yan sanda inda daga nan aka fara bincike a kai.
Yanzu dai an tsare ita wannan yarinya a ofishin ‘yan sanda har sai an kammala bincike a kai.
Discussion about this post