Dalilin da ya sa Buhari ya fasa gajeruwar hutun sa

0

Idan ba a manta ba tun a ranar Lahadi da ya gabata ne tawagar shugaban Kasa suka fara yin gaba zuwa Benin, babbar birnin jihar Edo domin shirin kaddamar da tashar wutar lantarki da shugaba Buhari zai yi. Sai dai kash, bayan wasun su sun riga sun isa garin Benin sai kuma a ka aika da sako da duk su dawo cewa Buhari ya canja shawara.

Bayan wannan tasha da shugaba Buhari zai kaddamar, zai dan yi ‘yar gajeruwar hutu a garin Daura.

Dalilin da ya sa shugaban kasa ya dakatar da wannan balaguro da zai yi da hutu kuwa shine domin ci gaba da ganawa da yake yi da hafsoshin sojin Najeriya da hukumomin tsaron kasa domin a gano inda aka samu baraka da ya kai ga kisan da aka yi wa daruruwan sojojin Najeriya a makon da ya gabata.

Buhari zai ci gaba da zama a fadar gwamnati domin ci gaba da wannan ganawa har sai an sami matsaya game da matsalolin tsaro da ake fama dasu a Najeriya a kwanakin nan da kuma sabon salon hare-hare da Boko Haram suka tsananta kan sojojin Najeriya a jihar Barno.

Share.

game da Author