Dalilan da ya sa na fice daga PDP na koma PRP – Hafiz Abubakar

0

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar ya koma jam’iyyar PRP daga PDP.

Da yake sanar da batun canja shekar tasa Hafiz ya bayyana cewa ya yanke shawarar haka bayan cin fuska da jam’iyyar PDP ta yi masa a jihar.

Idan ba a manta ba Hafiz Bello ya sauka daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje inda ya bi sanata Rabiu Musa KWankwaso zuwa jam’iyyar PDP.

Bello ya ce irin yadda aka gudanar da zabukan kujerun ‘yan takara a jam’iyyar na daga cikin dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar.

” Ace wai duk da irin gudunmuwar da na bada a jam’iyar PDP wai in kasa samun koda kujera guda ne na wakili a majalisa.

Bayan haka ya koka da rashin adalcin da aka nuna masa a jam’iyyar da ya sa kawai ya yanke wa kansa hukuncin komawa jam’iyyar PRP.

ya ce da shi da magoya bayan sa kaf zasu koma PRP sannan ya bayyana farincikin sa bisa yadda shirin fidda ‘yan takara yake a ajam’iyyar PRP din.

Share.

game da Author