Dalilai 10 da yasa mata ke bukatan yawan saduwa da mazajen su akai-akai – Likita Maimuna

0

Kwararriyar Likita Maimuna Kadiri ta hori mata da su rika yawan saduwa da mazajen su domin samun annashuwa da karin kafiya a jikin su.

Maimuna wadda ita ce babban likita kuma shugaban kanfanin (Pinnacle Medical Services) ta hori mata da su rika yawan saduwa da mazajen su akai-akai domin samun waraka ga matsalolin rayuwa. Sannan tace hakan na kara kaifin kwa-kwalwar mace.

” A matsayin mu na mata dole ne fa mu rika kusantar mazajen mu akai-akai ko don zama cikin koshin lafiya da lafiyar kwakwalwa. Mace kan fada cikin halin damuwa da kakanikayi idan bata samun saduwa da na miji yadda ya kamata.

” Matan da kan sadu da mazajen su akai-akai sun fi rashin fadawa cikin halin damuwa da matsalolin kiwon lafiya fiye da wadanda ba haka ba. Bayan haka akan samu dankon soyayya a tsakanin miji da mata.

Maimuna ta ce mata su dage da saduwa da mazajen su domin hakan ma na warkar da matan dake yawan ciwon kai sannan kuma yakan sa a ji dadin jiki matuka.

1 – Hakan na sa a samu waraka daga yawan yin ciwon kai

2 – Yana kaifafa kwakwalwar mace

3 – Yana kara dankon soyayya a tsakanin masoya

4 – Ya kan yaye damuwa.

5 – Yana kawar da yawan tunane-tunane

6 – Yana gyara jikin mace

7 – Ana samun nagartaccen barci da lafiya

8 – Ana zama cikin farinciki a ko da yaushe

9 – Fatar mace zai rika sheki da kyaun gani

10 – Yana karkato da ra’ayin namiji ga mace a samu zaman lafiya da so ga juna.

Share.

game da Author