Shugaban makarantar Sakandare na mata dake Dapchi jihar Yobe Adama Abdulkarim ta bayyana cewa dalibai sun fara karatu a makarantar tun bayan rufe ta.
Adama ta bayyana cewa a yanzu haka malamai da daliban makarantar kashi 80 bisa 100 sun dawo.
Idan ba a manta ba a ranar 19 ga watan Fabrairu ne ‘yan Boko Haram suka sace dalibai mata 110 daga wannan makaranta dake Dapchi.
Bayan wata daya da sace su Boko Haram suka dawo da su sai dai tun a lokacin biyar daga cikin daliban sun rasu sannan har yanzu suna rike da guda daya mai suna Leah Sharibu.
” Mun nemo wasu mata da za rika zama da daliban a dakunan su bayan an kammala karatu sannan ‘yan sanda da civil Defence na nan a kullum domin samar da tsaro a makarantar.
A karshe Adama ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin bada tallafi kan tallafa musu wajen gyaran makarantar domin iyaye su sami karfin gwiwar dawo ‘ya’yan su karatu a makarantar.