Dakarun sojin Najeriya sun yi raga-raga da Boko Haram a Kukawa, jihar Barno

0

Rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa dakarun ta sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram a karamar hukumar Kukawa, jihar Barno.

Rundunar ta sanar da haka ne a shafinta na Twitter ranara Talata inda ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun yi ragaraga da da mayakan Boko Harama.

” A ranar Talata da misalin karfe takwas na dare dakarun sojin Najeriya suka fatattaki wasu ‘yan Boko Haram da suka yi kokarin shiga kauyen Cross-Kauwa dake karamar hukumar Kukawa.

Wannan nasara da rundunar ta samu ya auku ne sati biyu bayan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya sama da 100 a garin Metele.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata a kan haka ya fasa hutun da yake shirin dauka domin ganawa da manyan hafsoshin Najeriya don ganin irin haka bai sake aukuwa ba.

Bayan haka Shugaba Buhari ya kira ganawar gaggawa na duka kasashen dake kewaye da tafkin Chadi ranar 29 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author